Jami'an tsaro a jihar California ta Amurka sun kama wani mutum ɗauke da bindiga a filin wasan golf mallakin Shugaban Amurka, Donald Trump, gabanin ziyararsa domin halartar wani taron tara kuɗaɗe na Jam'iyyar Republican.
Masu bincike sun bayyana cewa mutumin, mai suna Jeanine John Tael, mai shekaru 38, an kama shi ne a filin wasan golf da ke Rancho Palos Verdes, tare da bindiga da kuma wasu alburusai da ake zargin haramtattu ne.
A cewar 'yan sanda, an ga mutumin yana yawo a sassa daban-daban na filin wasan, yana ɗaukar hotuna da bidiyo tare da lura da shirye-shiryen tsaro da ake yi kafin isowar Shugaba Trump.
Rahotanni sun ce an kama shi ne ranar Lahadi, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun jami'an tsaro yayin da yake fuskantar zarge-zargen ɗauke da bindiga a ɓoye ba tare da izini ba da kuma mallakar haramtattun alburusai.
Jami'an tsaro sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin kasancewar mutumin a wurin da kuma ko akwai wata barazana da ya ke shirin haifarwa.