Sheikh Yahya Jingir ya bayyana cewa ba ya tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sai dai yana tallata abin da ya yi imani da shi na Musulunci.


Malamin ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba shi damar bayyana ra’ayinsa da kuma zaɓen ɗan takarar da yake so.


Sheikh Jingir ya jaddada cewa matsayinsa na bayyana ra’ayin siyasa yana cikin ’yancin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ɗan ƙasa.