Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya dauki nauyin karatun dalibai 830 da suka kammala karatun NCE a Community College of Education da ke Kano.
An gabatar wa daliban takardun shaidar kammala karatunsu ne a ranar Asabar, yayin wani bikin yaye dalibai da aka gudanar a zauren taro na SAS da ke Kano.
Mai magana da yawun Shekarau, Farfesa Sule Ya’u Sule, ya ce an fara shirin tallafin karatun ne a shekarar 2022, lokacin da Shekarau ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin bai wa matasa daga ƙananan hukumomi 15 na mazabar Kano ta Tsakiya damar samun ilimin koyarwa, inda aka ware dalibai 50 daga kowace ƙaramar hukuma, jimillar dalibai 750.
Farfesa Sule ya ƙara da cewa Shekarau ya kuma tallafa wa wasu dalibai 100 na Community College of Education waɗanda suka kasa biyan kuɗin makaranta, abin da ya sa jimillar waɗanda suka amfana da tallafin ta kai 850.
Daga cikin dalibai 850, 830 sun kammala karatunsu tare da karɓar takardun shaidar NCE, yayin da 15 suka samu carry-over, sannan biyar suka daina karatun.
A cewar Sule, Shekarau ya nuna farin cikinsa kan nasarar shirin, tare da sake jaddada ƙudurinsa na ci gaba da tallafa wa matasa domin samun ingantaccen ilimi.
Ya kuma ce lokacin da daliban suka kammala karatunsu ya zo daidai da lokacin da gwamnatin Jihar Kano ke shirin ɗaukar sabbin malamai aiki, yana mai fatan waɗanda suka kammala za su samu damar cin gajiyar wannan shiri.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya yaba wa Shekarau bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da haɓaka jarin ɗan Adam.
A cewar Farfesa Sule, Mataimakin Gwamnan ya kuma yi alƙawarin tattaunawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yiwuwar samar da guraben aikin yi ga wasu daga cikin sabbin waɗanda suka kammala NCE.
Bikin ya samu halartar manyan baki, ciki har da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, da Babban Limamin Kano, Farfesa Muhammad Sani Zahradeen, da sauran shugabannin siyasa, addini da al’umma.