Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta umarci rassanta da ke jami’o’i 20 da su fara shirye-shiryen shiga yajin aikin gama-gari, bisa zargin cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi sun gaza cika wasu daga cikin alƙawuran da suka ɗauka a yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyar a shekarar 2025.

ASUU ta ce ta bai wa gwamnatocin da abin ya shafa wa’adin makonni biyu domin su magance matsalolin da suka rage, kafin ɗaukar matakin yajin aiki.

Shugaban ASUU na shiyyar Kano, Dakta Abdulrazaq Ibrahim Fagge, ya ce an ɗauki matakin ne bayan taron uwar ƙungiyar da aka gudanar a Abuja, sakamakon ƙorafe-ƙorafen da suka fito daga wasu jami’o’i, musamman jami’o’in jihohi.

Ya ce duk da yarjejeniyar da aka cimma a Disambar 2025 kan sabbin alawus-alawus da kuma wasu sauye-sauye a tsarin gudanar da jami’o’i, har yanzu wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da abubuwan da suka amince da su ba.

A cewar ASUU, yayin da gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da nata ɓangaren yarjejeniyar tun daga Janairun 2026, wasu gwamnatocin jihohi sun gaza yin hakan.

Ƙungiyar ta zargi wasu gwamnatocin jihohi da fifita wasu ayyuka da take ganin ba su kai ilimi muhimmanci ba, tana mai cewa ba ta da shirin sake komawa teburin tattaunawa da gwamnati a halin yanzu, bayan shafe watanni takwas ana tattaunawa ba tare da samun gagarumin ci gaba ba.

ASUU ta yi gargadin cewa rassan jami’o’in da abin ya shafa za su shiga yajin aiki bayan cikar wa’adin makonni biyu, idan har ba a warware matsalolin da suke neman a magance ba.