Shugaban Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Kano (KanInvest), Dr. Muhammad Nazir Halliru, ya karɓi tawagar tsoffin shugabannin jam’iyyar PDP daga mazabu 11 na Ƙaramar Hukumar Nassarawa, waɗanda suka fice daga PDP suka koma jam’iyyar APC.

Tawagar ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana mai cewa matakin komawarsu APC ya samo asali ne daga irin nasarori da ayyukan raya jihar da gwamnatin ke aiwatarwa.

Da yake magana a madadin ƙungiyar, Shugaban tsoffin shugabannin PDP da suka koma APC, Alhaji Sani Suleiman Dakata, ya ce sun yanke shawarar mara wa gwamnatin jihar baya ne domin tallafa wa manufofi da shirye-shiryenta, musamman waɗanda suka shafi inganta rayuwar jama’a da bunƙasa tattalin arzikin Kano.

Ya ce ci gaban da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke samu ya ƙara musu kwarin gwiwar shiga APC domin bayar da gudunmawarsu wajen cimma manufofin ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

A nasa jawabin, Dr. Muhammad Nazir Halliru ya yaba da matakin da tsoffin shugabannin suka ɗauka, yana mai cewa hakan na nuna balagar siyasa da hangen nesa.

Ya ce sun fahimci muhimmancin ajandar “Kano First” ta Gwamna Abba Kabir Yusuf, wadda ta mayar da hankali kan sanya muradun jama’a, ci gaban jihar da walwalar al’umma a tsakiyar manufofin gwamnati.

Dr. Nazir ya jaddada cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki, inganta walwalar jama’a da samar da yanayi mai kyau ga zuba jari da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma buƙaci tsoffin shugabannin PDP ɗin da su ci gaba da wayar da kan jama’a kan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar, musamman ajandar Kano First.

A ƙarshe, ya yi musu fatan alheri a sabuwar tafiyarsu ta siyasa, yana mai cewa goyon bayansu zai taimaka wajen ƙara bunƙasa Jihar Kano.