Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da ƙarfin da za ta iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 saboda matsalolin cikin gida da ke ci gaba da addabarta.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce abin da ya kamata jam'iyyar ta fi mayar da hankali a kai a yanzu shi ne ƙoƙarin lashe wasu gwamnoni da sauran muƙaman jihohi, tare da sake gina jam'iyyar domin tunkarar zaɓen shekarar 2031.
Ya ce, a halin yanzu, zai yi matuƙar wahala PDP ta gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai ƙarfi saboda rikice-rikicen cikin gida da har yanzu ba a warware su ba.
A cewarsa, "Tun da daɗewa nake faɗa cewa PDP ba za ta iya cin zaɓen shugaban ƙasa yanzu ba. Abin da muke yi shi ne ƙoƙarin lashe wasu muƙaman jihohi da kuma shirya jam'iyyar domin zaɓen 2031."
Wike ya jaddada cewa sai jam'iyyar ta fara magance matsalolinta na cikin gida da sake haɗa kan mambobinta kafin ta yi tunanin fafatawa da ƙarfi a babban zaɓen ƙasa.