Gwamna Uba Sani ya iso Afaka wurin aza harsashin fara aikin titin kilomita 122 daga Kaduna - Birnin Gwari. Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakiyar gwamna Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ministar ayyuka Sanata Engr. David Nweze Umahi, Karamin Ministan Ayyuka Barr. Bello M. Goronyo, Ministan Muhalli Balarabe Abbas Lawal, Ministan Gidaje da Raya Birane shi ne Engr. Muttaqha Rabe Darma, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa da sauran su, Ibrahim Masari, tsohon gwamna Ramalan Yero, Sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bamalli da sauran manyan baki.
In ba a manta ba, makonnin da suka gabata, Gwamna Uba Sani ya sanar da cewa Shugaba Tinubu ya amince da Naira biliyan ₦178.12 don gina aikin hanyar Kaduna-Birnin Gwari. Domin a fara aikin nan take, an riga an ware Naira biliyan ₦100 don tabbatar da an fara aiki ba tsayawa.
Wannan aikin babbar hanyar za ta tashi ne daga Mando a Kaduna zuwa garin Birnin Gwari. Kowa yana sane wannan hanya ta daɗe tana neman irin wannan ɗaukin daga gwamnati.

Abin farin ciki shi ne wannan aikin hanyar za a yi da sabuwar fasaha ce ta aiki da kankare wato, Continuously Reinforced Continental Pavement (CRCP) - wani tsari ne mai ƙarfin gaske na shimfida hanya da kankare na siminti da duwatsu wanda masana suka ce zai iya ɗaukar har zuwa shekaru 100.
Samun amincewa na aikin hanya, wata babbar nasara ce ga da ke nuna tsaro ya inganta a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Uba Sani. Birnin Gwari a da wuri ne da ba a iya zuwa. Cikin yardar Allah yanzu haka, al'amura na dawowa: kasuwannin da aka rufe tsawon sama da shekaru goma yanzu an buɗe suna ci. Gonakin da aka yi watsi da su a baya saboda matsalar tsaro, yanzu ana nomawa, sannan kuma ana kan gina wata hanya mai tsawon kilomita 36 daga Bagoma zuwa Gagumi.
A ƙarshe bukin fara wannan aikin a yau ya nuna ƙoƙarin Gwamna Uba Sani. Kuma wannan ya nuna irin kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna don samar da cigaba a Jihar Kaduna.
#WokingForKaduna