Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku na tsawon watanni uku bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati, amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba da wasu laifukan gudanarwa.

Shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Alhassan Salisu na Bebeji da Abubakar Mustapha na Rogo.

Matakin ya biyo bayan amincewar majalisar da rahoton Kwamitin Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, wanda shugabansa, Aliyu Muhammad, ya gabatar a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Ismail Falgore.

Rahoton kwamitin ya bayyana cewa an samu zargin karkatar da kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa a Ƙaramar Hukumar Bagwai.

A Ƙaramar Hukumar Bebeji kuwa, kwamitin ya ce ya gano zarge-zargen amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba, take dokokin bayar da kwangila da aiwatar da su, sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa'ida ba da kuma karkatar da kuɗaɗen jama'a.

Rahoton ya kuma zargi shugaban ƙaramar hukumar Bebeji da tilasta wa wasu 'yan kwangila tura kuɗaɗen kwangilolinsu zuwa wasu asusun banki da ake zargin shi ne ya zaɓa.

A Ƙaramar Hukumar Rogo kuma, kwamitin ya ce shugaban ƙaramar hukumar na fuskantar zarge-zargen yin karan-tsaye ga manufofin gwamnati, amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba da kuma karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan gina hanyoyin karkara da samar da wutar lantarki a al'ummomin Unguwar Dawa da Hausawa Fulani.

Bisa waɗannan zarge-zarge, kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin uku har sai an kammala cikakken bincike, yana mai kafa hujja da sashe na 128 da na 129 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999.