Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace ya faɗaɗa ayyukansa a yankin Afirka bayan ƙaddamar da sabbin hanyoyin zirga-zirga daga Legas zuwa Bamako a ƙasar Mali, Conakry a Guinea, Douala a Kamaru da kuma Libreville a Gabon.
Kamfanin ya bayyana cewa ƙaddamar da waɗannan sabbin hanyoyi na da nufin ƙarfafa haɗin kai da sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji tsakanin ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Air Peace ya kuma ce sabon tsarin zai ƙara bunƙasa matsayin Legas a matsayin babbar cibiyar haɗa zirga-zirgar jiragen sama ta yankin, tare da samar da ƙarin damar kasuwanci, yawon buɗe ido da bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka.