Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa babu ɗan siyasar da zai yi niyyar ƙarfafa abokin hamayyarsa a lokacin fafatawar siyasa, domin kowa yana ƙoƙarin kare muradunsa da bunƙasa tasirinsa.

Wike ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja, yayin da yake martani kan kalaman Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa, "komai halal ne a siyasa" (all is fair in politics).

Ministan ya ce a tsarin siyasa, abin da 'yan siyasa ke yi shi ne neman hanyoyin da za su ƙarfafa matsayinsu da kuma cimma manufofinsu, ba wai su taimaka wa abokan hamayyarsu su fi ƙarfi ba.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan kalamai ya kamata a fahimce su a mahangar yadda siyasa ke gudana, inda gasa da neman goyon bayan jama'a ke kasancewa ginshiƙin tsarin dimokuraɗiyya.