Manyan kamfanonin mai a duniya sun ba da rahoton ribar da ba su taɓa samu ba, sakamakon tashin farashin danyen mai da ya biyo bayan rikicin Iran.
Kamfanin Saudi Aramco, wanda shi ne mafi girma wajen samar da danyen mai a duniya, ya bayyana cewa ribarsa ta ƙaru da kashi 44 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar nan. Hakan ya faru duk da rufe Mashigar Hormuz da Iran ta yi da kuma hare-haren mayaƙan Houthi kan jiragen ruwan Saudiyya a Tekun Maliya.
Haka kuma, manyan kamfanonin makamashi na ƙasashen Yamma guda biyar—BP, Chevron, ExxonMobil, Shell da TotalEnergies—sun sanar da haɗaɗɗiyar riba da ta kai kusan dala biliyan 47.
A cewar rahotanni, farashin danyen mai ya riƙa yin tashin gwauron zabi da sauka tun bayan ɓarkewar rikicin, inda farashin gangar mai nau'in Brent ya haura dala 120 kafin daga bisani ya fara raguwa bayan an fara hasashen yiwuwar tattaunawar sasanta rikicin.
A nasa ɓangaren, Shugaban Amurka Donald Trump ya soki manyan kamfanonin man fetur, yana zarginsu da cin gajiyar yaƙin wajen tara riba mai yawa. Ya kuma buƙace su da su rage farashin mai domin sauƙaƙa wa jama'a matsin tattalin arziki.