Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tawagar Najeriya murnar bajintar da ta nuna a Gasar Commonwealth da aka gudanar a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, bayan da ta lashe jimillar lambobin yabo 24.
Tawagar Najeriya ta samu lambobin zinariya 10, azurfa 7 da tagulla 7, lamarin da ya sanya ƙasar cikin waɗanda suka yi fice a gasar.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba wa 'yan wasan bisa jajircewa, ƙwazo da kuma nuna kishin ƙasa, yana mai cewa sun ɗaga darajar Najeriya a idon duniya.
Shugaban ya bayyana cewa nasarorin da tawagar ta samu shaida ce ta irin ƙoƙari, sadaukarwa da kuma horon da 'yan wasan suka yi domin kai wa wannan matsayi.
Ya kuma yabawa shugabannin Kwamitin Olympics na Najeriya da Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa bisa ci gaba da tallafa wa 'yan wasa da kuma bunƙasa harkokin wasanni a ƙasar.
Tinubu ya ce ƙwarewar da 'yan wasan suka samu a gasar za ta kasance tubalin samun manyan nasarori a sauran gasa na duniya a nan gaba, tare da zama abin ƙarfafawa ga matasan Najeriya.
A ƙarshe, Shugaban Ƙasa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin wasanni, ta hanyar inganta cibiyoyin horaswa, ƙarfafa tsarin bunƙasa wasanni da samar da ƙarin damammaki ga hazikan 'yan wasa domin su yi fice a matakin nahiyar Afirka da na duniya.