Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bai wa Malam Usman Aliyu, mijin marigayiya Ummulkhairi, malamar Islamiyyar da aka kashe ta hanyar ƙonawa a Maraban Jos, kyautar gida domin taimaka masa ya sake gina rayuwarsa bayan wannan mummunan lamari.
Marigayiya Ummulkhairi ta rasa ranta ne bayan wasu matasa sun kai mata hari bisa zargin satar yara, zargin da ya jawo aka banka mata wuta har ta mutu.
Gwamna Uba Sani ya miƙa takardun gidan ga Malam Usman Aliyu ne yayin da ya kai masa ziyarar godiya tare da rakiyar fitaccen malamin addini, Sheikh Haliru Maraya.
Gwamnan ya bayyana cewa tun bayan aukuwar lamarin, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiyar, inda ya tabbatar musu cewa gwamnatin jihar ba za ta tsaya kan kalaman jaje kawai ba, sai ta ɗauki matakan tallafa musu.
Ya ƙara da cewa baya ga ba iyalan gidan zama da tallafin kuɗi, gwamnatin jihar ta kuma ɗauki nauyin karatun 'ya'yan marigayiyar domin tabbatar da cewa sun samu kyakkyawar makoma duk da rashin mahaifiyarsu.