Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Tawagar Najeriya murnar bajintar da ta nuna a Gasar Commonwealth da aka gudanar a birnin Glasgow na ƙasar Scotland.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba wa 'yan wasan bisa nuna jajircewa, ƙwazo, ladabi da nagartar da ke bayyana ruhin ɗan Najeriya.
Shugaban ya yabawa tawagar saboda ɗaga tutar Najeriya cikin mutunci da alfahari, yana mai cewa lambobin yabo 24 da tawagar ta samu—zinariya 10, azurfa 7 da tagulla 7—shaida ce ta irin ƙoƙari, sadaukarwa da jajircewar 'yan wasan.
Ya bayyana cewa ƙwarewar da kowane ɗan wasa ya samu a gasar za ta kasance ginshiƙi na samun manyan nasarori a gasa ta ƙasa da ƙasa nan gaba, tare da ƙarfafa matasa 'yan Najeriya su rungumi ƙimar sadaukarwa da yi wa ƙasa hidima.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa shugabannin Kwamitin Olympic na Najeriya (NOC) da Hukumar Wasanni ta Ƙasa bisa ci gaba da ƙoƙarinsu wajen bunƙasa harkokin wasanni da tallafa wa 'yan wasa.
A ƙarshe, Shugaban ya buƙaci 'yan wasan da su ci gaba da mayar da hankali kan neman ƙarin nasarori, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a bunƙasa wasanni, ƙarfafa cibiyoyin wasanni, inganta wuraren horaswa da kuma samar da ƙarin damammaki ga hazikan 'yan wasa domin su yi fice a matakin nahiyar Afirka da na duniya.