Rahotanni sun nuna cewa hukumomin Canada sun ƙi amincewa da takardar izinin shiga ƙasar da ɗan wasan tsakiyar Ghana, Thomas Partey, ya nema, lamarin da zai hana shi buga wasan farko na Ghana a gasar cin kofin duniya da za ta yi da Panama a birnin Toronto ranar 17 ga Yuni.
Hukumar FIFA ta tabbatar da cewa Partey ba zai samu damar tafiya daga sansanin tawagar Ghana da ke Boston a Amurka zuwa Canada ba, bayan da gwamnatin Canada ta ƙi amincewa da buƙatar takardar izinin shigarsa. FIFA ta jaddada cewa ba ta da hannu a harkokin ba da biza, domin hakan na ƙarƙashin ikon ƙasashen da ke karɓar baƙuncin gasar.
Rahotanni sun ce duk da cewa ba zai buga wasan da Panama ba, Partey na iya kasancewa cikin tawagar Ghana a sauran wasannin rukuni da za a buga a Amurka, ciki har da wasannin da za ta yi da Ingila da Croatia.
Wannan mataki ya zama babban ƙalubale ga Ghana, wadda ke fatan amfani da gogewar Partey a wasannin rukuni na gasar cin kofin duniya.