Ɗan siyasa kuma ɗan majalisar dokokin Afirka ta Kudu, Julius Malema, ya bayyana hare-haren ƙiyayya ga baƙi da aka kai kwanan nan a ƙasar a matsayin waɗanda "gwamnati ta ɗauki nauyinsu".

Malema ya zargi ƴansanda da sauran hukumomin gwamnati da gaza ɗaukar matakan da suka dace domin dakatar da ayyukan tsoratarwa, cin zarafi da kuma hare-haren da ake kai wa baƙi a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce rashin ɗaukar mataki cikin gaggawa daga hukumomi ya ba wasu damar ci gaba da kai hare-hare ba tare da fargabar hukunci ba.

Kalaman na Malema na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda hare-haren ƙiyayya ga baƙi ke ƙaruwa a wasu yankunan Afirka ta Kudu, lamarin da ya haifar da kira ga gwamnati da ta ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin mazauna ƙasar ba tare da la’akari da asalin ƙasarsu ba.