Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun samu nasarar dakile wani yunkurin kutsen ƴan ta’adda tare da lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.
A cewar rundunar, matakin na daga cikin ƙoƙarin da take yi na raunana ƙarfin ƴan ta’adda da hana su ci gaba da kai hare-hare a yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa a jihar Borno, sojoji sun yi gaggawar mayar da martani bayan sun hango motsin ƴan ta’adda da ke ƙoƙarin kusantar cibiyar horas da sojoji da ke Buni Yadi a ranar 9 ga Yuni.
Rundunar ta ce dakarunta sun buɗe wa maharan wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa, yayin da aka kashe wasu daga cikinsu. An kuma gano gawarwakin ƴan ta’adda biyu da babur guda a wurin da aka fafata.
A wani samame na daban, sojoji sun kama wasu mutane da ake zargi da samar wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP kayan aiki a yankin Damboa.
Rundunar sojin ta jaddada cewa waɗannan nasarori na nuna aniyarta ta katse hanyoyin tallafa wa ƴan ta’adda da kuma tabbatar da tsaro da dawowar zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.