An sanar da cewa za a binne tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, a ranar 8 ga Yulin 2026, watanni uku bayan rasuwarsa sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai masa.

Sanarwar da ofishin wallafa ayyukansa ya fitar ta ce za a fara gudanar da jana’izarsa a ranar 4 ga Yuli a Tehran, kafin a binne shi a harabar Masallacin Imam Reza da ke Mashhad a ranar 8 ga Yuli.

Haka kuma, za a gudanar da jana’izar wasu daga cikin ’yan uwansa da suka mutu tare da shi a hare-haren a biranen Tehran, Qom da Mashhad.

Jami’ai sun bayyana cewa ana sa ran jana’izar za ta tara miliyoyin mutane, inda aka tsara gangamin jama’a na kwanaki uku da sauran shirye-shiryen musamman domin karrama marigayin.