A ranar Asabar, 13 ga Yunin 2026, tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe, ya rasu yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Gwamnatin jihar Katsina ce ta tabbatar da rasuwarsa ta cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Nasiru Mu'azu, ya fitar. Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon ta'azzarar ciwon siga da hawan jini da yake fama da su a lokacin da yake tsare.
A cewar gwamnatin jihar, an yi ƙoƙari tare da jami'an tsaro domin ceto Manjo Janar Rabe cikin ƙoshin lafiya, sai dai ba a samu nasarar kuɓutar da shi da rai ba.
Rasuwar tsohon hafsan sojan ta haifar da alhini a tsakanin iyalansa, al'ummar jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana mutuwar tasa a matsayin babban rashi ga jihar da ƙasa, tare da miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin.