Tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), ya rasu yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina.
Gwamnatin Jihar Katsina ce ta tabbatar da rasuwar tasa ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida ya fitar. Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon tsanantar rashin lafiyar ciwon suga da hawan jini da yake fama da su yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga.
A cewar gwamnatin jihar, an yi kokari sosai tare da hadin gwiwar jami’an tsaro domin ceto shi cikin koshin lafiya, amma abin takaici, kokarin bai yi nasara ba.
Rasuwar Janar Rabe ta jefa iyalansa, al’ummar Jihar Katsina da ma Najeriya baki daya cikin jimami da alhini.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar da kasa baki daya, tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Ya kuma jaddada bukatar kara karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da al’umma domin magance matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar yankuna da dama a kasar nan.
A kwanakin baya ne dai wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da Janar Abubakar Rabe da matarsa a Katsina, inda daga bisani aka ga su a wani faifan bidiyo suna rokon hukumomin Najeriya da su taimaka wajen ceto su.