Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol, hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan same shi da laifin bayar da umarnin aika jirage marasa matuƙa zuwa Koriya ta Arewa.

Rahotanni sun ce dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara tsami ne a shekarar 2024 bayan wani jirgi marar matuƙi ya watsa takardu a cikin birnin Pyongyang, babban birnin Koriya ta Arewa.

Kotun ta bayyana cewa matakin na daga cikin wani yunƙuri na tunzura Koriya ta Arewa ta mayar da martani ta hanyar kai hari, domin samar da dalilin aiwatar da matakan mulkin soja da aka tsara.

Tun bayan tsige shi daga mulki sakamakon yunƙurinsa na ayyana dokar mulkin soja a watan Disamban 2024, Yoon ya fuskanci jerin shari’o’i da suka shafi cin zarafin kundin tsarin mulki da sauran laifuka.

A watan Fabrairu, an same shi da laifin tayar da ƙayar baya, inda kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Sabon hukuncin daurin shekaru 30 na daga cikin shari’o’in da ake ci gaba da yi masa bayan ficewarsa daga mulki.