Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da ƙaunar ƙasarsu duk da ƙalubalen da take fuskanta, musamman matsalar tsaro.

A jawabinsa na ranar Dimokraɗiyya, Tinubu ya bayyana cewa yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 27 na mulkin dimokraɗiyya ba tare da tangarɗa ba, an samu wasu abubuwa masu tayar da hankali da suka haɗa da sace ɗalibai a jihohin Oyo da Borno.

Shugaban ya jaddada cewa dimokraɗiyya ba za ta yi ƙarfi ko ta cimma manufarta ba idan babu ingantaccen tsaro, yana mai cewa hakan ne ya sa gwamnatinsa ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Ya ce gwamnati ta ayyana ta-baci kan matsalar tsaro tare da amincewa da ɗaukar sabbin jami’an ‘yan sanda sama da 50,000 da kuma dubban sojoji domin ƙarfafa ayyukan tsaro.

A ƙarshen jawabinsa, Tinubu ya karrama marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola (M.K.O. Abiola), wanda ake tunawa da shi a ranar Dimokraɗiyya, yana mai cewa ya kasance jagora wanda ya samu goyon bayan al’ummar Najeriya daga kowane ɓangare na addini da al’adu.