Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya magantu kan ziyarar da ya kai garin Ibadan a ƙarshen shekarar da ta gabata, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo baya cewa yana ƙoƙarin yaɗa manufofin addinin Musulunci a Jihar Oyo.
Gumi ya jaddada cewa babu wanda zai hana shi ziyartar ko'ina a cikin ƙasar nan, yana mai cewa ba wata ƙungiyar Musulmi ko wani mutum daga yankin Kudu maso Yamma ne ya gayyace shi ba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, ya ce ya je Ibadan ne a matsayin wakilin malaman addinin Musulunci na Arewacin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne kwana guda bayan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo ya musanta ikirarin cewa masu garkuwar sun buƙaci a aiwatar da dokar Shari’a a jihar a matsayin wani sharadi na sakin waɗanda suka yi garkuwa da su.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa shugaban makarantar Community High School da ke Esiele a Jihar Oyo, Misis Rachael Alamu, yayin da take tsare a hannun masu garkuwa a wani bidiyo da ya bazua shafukan sada zumunta, ta ce maharan sun bayyana cewa ba su taɓa neman a kafa dokar Shari’a ko a biya su kuɗin fansa na Naira biliyan ɗaya ba kamar yadda wasu ke yaɗawa.
Maimakon haka, ta ce abin da suka nema shi ne a saki abokan hulɗarsu da ke tsare a hannun hukumomin Najeriya.