An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar kusan mutum 40 a wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru a Najeriya.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda fasinjoji da dama suka samu raunuka daban-daban.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ƙasar ya sauka daga kan layin dogo ne yayin da yake kan hanyarsa daga Warri zuwa Itakpe, a yankin Agbor na jihar Delta da ke kudancin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da NRC ta fitar, ta ce ta tura jami’an kai ɗaukin gaggawa tare da sauran hukumomin da abin ya shafa zuwa wurin da hatsarin ya auku domin gudanar da ayyukan ceto da bayar da taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.

Sai dai wasu shaidu sun bayyana fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu na iya zarce mutum ukun da aka tabbatar a hukumance.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ika North-East, Monday Odigwe, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa fiye da fasinjoji 35 ne suka jikkata, kuma ana ci gaba da kula da su a asibitoci daban-daban.

Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da jajanta wa waɗanda suka jikkata.

Hatsarin ya sake janyo hankali kan matsalolin da ke addabar harkar sufurin jiragen ƙasa a Najeriya, inda ake yawan samun saukar taragai daga kan layin dogo da kuma tsaikon ayyukan jiragen a wasu hanyoyi.

A watan Agustan 2026 ma, wani jirgin ƙasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya fuskanci matsala bayan ya sauka daga kan layi jim kaɗan bayan barinsa tashar Abuja.