Shugaban Jam’iyyar PRP Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina duba yanki ko shiyya wajen zaɓen shugabanni, maimakon haka su zaɓi mutanen da ke da ƙwarewa, nagarta da hangen nesa.
Baba-Ahmed ya yi wannan kira ne cikin shirin kamfanin dillancin Labarai na kasa NAN, mai taken Personality Interview Series a ranar Talata a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban na PRP ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan Cross River State, Donald Duke, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar domin zaɓen gama gari na shekarar 2027.
Yayin da yake bayyana cewa jam’iyyar ta yi watsi da siyasar rabon mulki bisa shiyya da kuma tunanin cewa wani yanki ne ke da haƙƙin samar da shugaba, Baba-Ahmed ya ce matsalolin da ƙasar ke ci gaba da fuskanta na buƙatar shugabanni masu ƙwarewa da nagarta, ba wai ’yan takarar da aka zaɓa kawai saboda yankin da suka fito ba.