Fitaccen lauya mai fafuktukar kare hakkin Dan adam Barista Abba Hikima, ya wallafa wannan sharawa ce a shafinsa na Facebook, kwana guda bayan da hukumar 'yan sanda ta jihar Kano tayi baje kolin wasu matasa masu dunbin yawa data kama Kan aikata laifuka daban daban a jihar.
Hikima ya kara da cewa, idan har kotu ta tabbatar da laifin da ake zargin matasan da aikatawa, to mai makon a mika su gidan Gyaran hali, a Kai su wani fili ko gona su yi noma wasu kuma su share gari. Musamman ma waɗanda basu yi nisa a harkar ba.
Inda ya cigaba da cewa yana yabawa jami’an yan sanda kan ƙoƙarinsu na kamo waɗannan matasan kusan 340 da ake zargi da ayyukan daba da shaye-shaye, cikin kwanaki 3.
"Ina kyautata zaton idan suka dore a wannan layin zamu samu saukin al’amura".
Kana ya yi Kira ga gwamnati tayi duk mai yiwuwa wajen samawa matasa aikin yi, ilimi, sana’a da kyakkyawan fata a rayuwa.