Ƙungiyar Hezbollah ta bayyana cewa ta harba jerin makamai masu linzami kan tarin motocin sojin Isra’ila tare da dakarunsu da ke kudancin Lebanon da safiyar yau.

A cikin wani saƙo da ta wallafa a manhajar Telegram, ƙungiyar ta ce ta kai farmakin ne kan wani taron sojojin Isra’ila a wajen garin Beit Yahoun da ke kudancin ƙasar.

Hezbollah ta bayyana harin a matsayin martani ga abin da ta kira karya yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan ƙauyukan kudancin Lebanon.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Isra’ila ba ta fitar da wani bayani ba kan lamarin, kuma ba a tabbatar da girman ɓarnar da harin ya haifar ba ko adadin waɗanda suka samu raunuka.

A halin da ake ciki, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, inda suke cewa suna yin hakan ne domin hana Hezbollah ci gaba da kai farmaki kan arewacin Isra’ila.