Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yabawa jami’an tsaro bisa nasarar ceto mutane 360 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke jihar Borno .
Atiku ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara, yana mai cewa hakan ya kawo ƙarshen wahalar da waɗanda aka sace da iyalansu suka shafe watanni suna fuskanta tun bayan sace su a watan Maris.
Ya kuma yabawa rundunar soji, musamman dakarun Operation HADIN KAI, da sauran hukumomin tsaro da suka taka rawa wajen gudanar da aikin ceton.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce idan aka samar wa sojoji kayan aiki da jagoranci mai ƙarfi, za su iya kawo ƙarshen matsalar ta’addanci da ta addabi ƙasar nan kusan tsawon shekaru 20.