Hukumar Bunƙasa Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) ta yi gargaɗi ga manoma da al’ummar jihar kan wasu mutane da ke amfani da sunanta wajen karɓar kuɗi da sunan samar da tallafin noma.
Shugaban hukumar, Dakta Farouk Ahmad Kurawa, ya bayyana cewa an gano wasu na karɓar kuɗi daga manoma, musamman a karkara, suna alƙawarin samar musu da taki, iri da sauran kayan aikin gona.
Hukumar ta bayyana cewa ba ta karɓar kuɗi daga manoma domin samun tallafin gwamnati ko wani taimako, tare da cewa duk masu yin hakan ƴan damfara ne.
KNARDA ta buƙaci al’umma su yi hattara da irin waɗannan mutane, sannan su kai rahotonsu ga hukumomin tsaro ko hukumar idan sun ci karo da su.