Gwamnatin Tarayya ta sauya ranar fara jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya da ke son dawowa daga ƙasar Afirka ta Kudu, biyo bayan hare-haren kin jinin baki (xenophobia).


Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.


A cewar Ebienfa, an sauya ranar jigilar rukunin farko na waɗanda ke son dawowa daga Afirka ta Kudu, wanda tun farko aka tsara yi a ranar Litinin (yau), zuwa ranar Laraba saboda wasu matsalolin shirye-shirye da ba a yi hasashensu ba.


Ta ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da jiragen kwashe mutane guda biyar, kuma kamfanin jiragen sama mai zaman kansa na Najeriya, Air Peace, ne zai kula da jigilar


Ebienfa ta ƙara da cewa jirgi na farko, wanda ake sa ran zai ɗauki kusan fasinjoji 270, zai tashi daga birnin Johannesburg a yammacin ranar da aka sake tsarawa, bayan an kammala samun dukkan izini da sahalewar da ake buƙata domin jirgin.