Rundunar Hisbah ta Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da gwajin lafiya ga mutanen da za su amfana da shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shiryawa, wanda zai haɗa ma'aurata 3,000.


Mataimakin Babban Kwamandan rundunar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya bayyana cewa daga ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2026 za a fara aikin tantancewar, inda ake buƙatar duk masu neman shiga shirin daga ƙananan hukumomi 24 su jr ofisoshin Hisbah da ke yankunan su.


Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Rogo, Wudil, Tudun Wada, Warawa, Kibiya, Dawakin Tofa, Garun Malam, Kura, Dambatta, Karaye, Tsanyawa, Minjibir, Rimin Gado, Shanono, Kabo, Tofa, Rano, Bebeji, Ajingi, Gwarzo, Sumaila, Kiru, Takai da Madobi.


A cewar Dr Aminuddeen, gwajin zai haɗa gwajin cuta mai karya garkuwar jiki, ciwon hanta, daidaiton kwayoyin halitta (genotype), amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma gwajin ciki ga mata.