Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, a birnin Tehran.
Kafin ganawar tasu a daren jiya Asabar, Naqvi ya kuma gana da takwaransa na Iran, Eskandar Momeni.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce bayan ganawar, Naqvi ya bayyana cewa ya kai ziyara Tehran ne domin isar da wata “wasika ta musamman” da kuma wani “muhimmin sako” daga babban kwamandan rundunar sojin Pakistan da kuma firaministan ƙasar zuwa ga Mojtaba Khamenei.
Sai dai rahotannin ba su bayyana cikakken abin da sakon ko wasikar suka ƙunsa ba.