A wani ɓangare na yaƙi da ta’addanci, ƙasar Mali ta samar da wasu shingayen jami’an tsaro a cikin dazuka, kilomita 40-40 tsakanin su da cikin gari, waɗanda aka haramtawa fararen hula kusantar gurin.

Bayanai sun ce za’a samar da waɗannan shingaye ne a cikin dazukan ƙasar sama da 40, inda aka fi tsammanin ƴan ta’adda na samun mafaka.

Da yake bayani kan sabon tsarin yaƙi da ta’addancin, ministan tsaron ƙasar, ya ce duk wanda aka samu a kusa da wannan shinge, za’a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.

Wannan sabuwar dabara zata rage hare-haren kwanton bauna da ƴan ta’adda ke kaiwa sojoji ta hanyar sajewa cikin fararen hula har sai sun zo kusa da su.