Shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da kungiyar ci gaban Fulani ta Najeriya sun yabawa gwamnatin Jihar Kano kan kokarin da take yi na kwato filayen kiwo 371, Burtalai da sauran guraren makiyaya da aka mamaye a fadin jihar.
Shugabannin kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne a tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN), inda suka ce matakin zai taimaka wajen rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma.
Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na Jihar Kano, Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, ya ce mamaye filayen kiwo da hanyoyin dabbobi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa sabani tsakanin makiyaya da manoma.
Ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa bada umarnin da ya haramta sayarwa ko sauya fasalin filayen kiwo da hanyoyin dabbobi ba bisa ka’ida ba.