Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana ci gaba da daukar matakan magance matsalar zaizayar kasa da ta dade tana addabar al’ummar Bulbula da Gayawa, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da kawo cikas ga harkokin yau da kullum na mazauna yankunan.
Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar samar da mafita mai dorewa ga matsalar, duk da cewa mutane da dama sun yi imanin cewa magance ta abu ne mai matukar wahala.