Dakarun rundunar Operation Hadin Kai tare da dakaru na musamman sun ceto mutane 360, galibinsu mata da kananan yara, da ’yan ta’adda suka sace daga garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.


Kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne a yankin tsaunukan Mandara a ranar 6 ga Yuni, inda aka samu nasarar kubutar da wadanda aka sace tun bayan harin da aka kai wa al’ummar Ngoshe a watan Maris.


Sai dai ya ce jarirai biyu sun rasu yayin aikin ceton sakamakon wahalar hanya. An kuma kai wadanda aka ceto asibiti domin kula da lafiyarsu kafin a hada su da iyalansu.