Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi gargaɗi ga duk wanda ke taimaka wa ’yan bindiga ta hanyar ba su bayanai, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan ayyuka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Birnin Kebbi, bayan sake barkewar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar.
Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin dakile ayyukan masu tayar da ƙayar baya.
Nasir Idris ya jaddada cewa ba za a yi afuwa ga duk wanda aka kama yana ba ’yan bindiga bayanai ko wata gudummawa ba, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.