Majalisar dattijan Najeriya ta yi alƙawarin gaggauta ɗaukar mataki da kuma samun matsaya kan batun ƴan sandan jihohi, a dai-dai lokacin da matsalolin ta’addanci ke ƙaruwa a sassan ƙasar.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Majalisar Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.
A cewar sa lokaci yayi da ya kamata a kawo ƙarshen jan ƙafar da ake yi game da batun samar da ƴan sandan jihohi wanda zai taimaka wajen kawo ƙarshen wannan matsala, da kuma baiwa manoma damar ci gaba da harkokin su na noma.
Kwanaki uku da suka gabata, Majalisar ta sanar da komawa kan wannan batu, inda ake ci gaba da tafka muhawara, yayin da ta buƙaci haɗin kan ƴan Majalisar domin kawo ƙarshen wannan matsala.