Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da matarsa, sun ruko Gwamnati ta kawo musu dauki daga hannun masu garkuwa da mutane.
Koken nasu na cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna huɗu da daƙiƙa biyu da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ga tsohon janar din da matarsa tsaye suna isar da buƙatun masu garkuwa da Mutanen da suka yi garkuwa da su.
Da take magana a cikin bidiyon, matar tsohon hafsan sojin ta bayyana cewa masu garkuwar sun buƙaci a saki mutum uku daga cikin membobinsu da suka bayyana sunayensu a matsayin Sani da Aminu da Nasiru.
Masu garkuwar sun kuma buƙaci a mayar musu da dabbobin da suka ce an ƙwace musu.
A cewar matar, an kama mutum biyu daga cikin waɗanda ake tsare da su a Jikamshi, yayin da aka kama na ukun a jihar Kano.
Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da su taimaka wajen cika waɗannan buƙatu domin a samu sakin su.
Tsohon Janar ɗin, wanda ya yi taƙaitaccen jawabi a cikin bidiyon, ya yi kira da a yi ƙoƙarin samar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha'awar tattaunawa da zaman tare cikin lumana.