Mai bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya zargi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da hana El-Rufai samun kulawar lafiya yayin da yake tsare a hannunta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce El-Rufai ya koka kan matsalar ƙaiƙayi da kumburi a idanunsa, lamarin da ya sa ya nemi a kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa. Sai dai, a cewarsa, jami’an ICPC ba su amince da wannan buƙata ba.

Adekeye ya bayyana cewa an kai El-Rufai wani asibitin ido a ranar 4 ga watan Yuni, amma daga bisani matsalar idanunsa ta ƙara tsananta, abin da ya jefa iyalansa cikin damuwa.

Ya ce jami’an hukumar sun ga halin da idanun El-Rufai suke ciki, amma duk da haka ba su samar masa da ƙarin kulawar likita ba, abin da ya ce ya ƙara ta’azzara matsalar.

Haka kuma, ya zargi ICPC da bai wa iyalan El-Rufai bayanan da ya ce ba su dace ba, bayan da aka shaida musu cewa bai nemi ganin likita ba. Adekeye ya ce wannan bayani ba gaskiya ba ne.

Ya kuma yi ikirarin cewa akwai umarnin kotu da ke bai wa El-Rufai damar samun kulawar lafiya idan bukatar hakan ta taso, amma har yanzu ba a aiwatar da umarnin yadda ya kamata ba.

Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ICPC ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye domin mayar da martani kan zarge-zargen ba, yayin da batun ke ci gaba da jan hankalin jama'a.