Haryanzu ana cigaba tafka muhara kan matsalar tsaro a nakeriya musamman a yankin arewa maso gabashi da kuma arewa ta tsakiya sai kuma wasu jihohi dake yankin Kudu maso yammaci, musamman ma kan batun sace daliban karanta a Jihar Borno d akuma jihar oyo.
Wani rahota da BBC hausa ta wallaf a shafinta a ranar 5 ga watan Yunin 2026, ya fito karara da sanda aka fara sace a dalibai a najeiya.
Rahohon na BBC yace, ‘yan Najeriya sun fara samun labarin garkuwa ko kashewa dalibai ne a ranar 14 ga watan Afrilun 2014 sanda mayaƙan Boko Haram suka kai wani hari makarantar sakandaren mata da ke Chibok a jihar Borno, tare da sace dalibbai mata 276, labarinda ya girgiza duniya da har aka fito da shirin Bringback our girls. Inda daga bisani aka samu nasarar ceto da yawa daga cikin su.
A watan Mayun shekarar 2017 ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai guda shida daga makarantar Lagos State Model College da ke garin Igbonla a jihar Legas.
A zamanin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, a watan Fabrairun 2018 ƴan Boko Haram kai hari makarantar mata da ke garin Dapchi na jihar Yobe sannan suka sace ɗalibai 110 inda daga bias aka saki mutane 104 60 kuma suka rasa rayukansu. inda a watan Disamban 2020 aka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta maza da ke garin Ƙankara na jihar Katsina aka sace ɗalibai sama da 300, Sai dai daga bisani an samu nasarar ceto ɗaliban
Kazalika a ranar Talata 16 ga watan Fabrairun 2021 ne ƴanbindiga suka kai hari a makarantar sakandaren maza da ke garin Kagara a jihar Neja, inda aka kwashe dalibai 27 da ma'aikata uku haɗi da iyalansu su goma 12 kuma cikin watan Fabrairun 2021 ma ƴan bindiga sun kai hari makarantar kwana ta mata da ke garin Jangeɓe a jihar Zamfara wato GGSS Jangebe, inda suka sace kimanin ɗalibai 317. Sai kuma a ranar 30 ga watan Mayun 2021 ne ƴanbindiga suka sace ɗaliban makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko Islamic School da ke garin Tegina, inda suka sace ɗalibai kusan 150.
A ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne ƴanbindiga suka kutsa makarantar sakandire ta kwana ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da ɗalibai fiye da 120.
Masu garkuwar sun saki ɗalibai a hankali
A watan Maris na 2021 ne ƴanbindiga suka kutsa kwalejin horas da harkokin noma da gandun daji wato Federal College of Forestry Mechanisation da ke Afaja a ƙarnar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda suka sace ɗalibai kimanin 30.
A watan Afrilun 2021 ne kuma ake samun aukuwar satar ɗalibai a jihar Kaduna, inda ƴanbindiga suka kai hari a Jami'ar Greenfield mai zaman kanta da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka sace ɗalibai da dama.
A watan Yunin 2021 suka ƙaddamar da hari a makarantar ɗalibai ta FGC Yauri da ke jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da ɗalibai masu yawa.
Bayanai sun bayyana cewa ƴanbindigar sun ci ƙarfin ƴansandan da ke gadin makarantar sannan suka ƙwace motoci ƙirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba ɗaliban a ciki sannan suka tafi da su.
A watan Janairun 2023ne ƴanbindiga suka far wa makarantar firamare ta garin Alwaza da ke jihar Nassarawa inda suka yi awon gaba da ɗalibai guda shida da rahotanni suka ce shekarunsu ba su wuce bakwai da takwas ba.
Ƴan bindigar dai sun yi garkuwa da ɗaliban ne a kan hanyar ƴan makarantar ta zuwa makaranta da misalin ƙarfe bakwai na safe.
Ƴansanda sun ce sun ceto su bayan ƙaddamar da aikin ceto.
A watan Oktoban 2023 ne kuma ƴanbindiga suka sace kimanin ɗalibai biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina.
BBC ta gano cewa lamarin ya faru ne a cikin dare da misalin karfe biyu a ɗakunan kwanan da ɗalibai ke kamawa a wajen makarantar.
A watan Satumban 2023 ne ƴanbindiga suka kai hari a gidajen kwanan ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Gusau a yankin Sabon Gida da ke jihar, inda rahotanni suka nuna sun sace ɗalibai kusan 22.
Ƴan bindigar waɗanda suka isa unguwar Sabon Gida da tsakar dare, sun rinƙa harbe-harbe kafin su yi awon-gaba da ɗaliban.
A watan Maris na shekarar 2024 ne ƴanbindiga suka sace ɗaliban firamare da na sakandare kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
A watan Maris na shekarar 2024 ne ƴanbindiga suka tsallaka makatantar Islamiyya ta kwana, inda suka sace ɗalibai 15.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin da tsakar dare a daidai lokacin da ɗaliban suke kwance suna barci.
A wani harin da jaridar Premium Times ta ruwaito, an sace ɗalibai 26 a cibiyar Daarul Kitab da ke ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi.
A ranar Litinin 17 ga watan Nuwamban 2025 ne ƴanbindiga suka sace ƴan mata ɗalibai 25 daga makarnatar kwana da ke garin Maga na ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
A ranar Alhamis 20 ga watan Nuwamban 2025 ne wasu ƴanbindiga suka kutsa makarantar sakandire ta St. Mary's inda suka yi awon gaba da ɗaliban da ba tabbatar da yawansu ba.
Cikin wata sanarwa da cocin St. Mary's ta fitar ta ce maharan sun ƙaddamar da harin ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 3:00 na dare a cikin makarantar.
Cocin ta ce lamarin ya haifar da tashin hankali da ruɗani a cikin hotuna.
Haka kuma cocin ta ce ta yi matuƙar damuwa da harin, tare da yin Allah wadai da shi da kuma kiran al'umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.
A watan Mayun 2026 ne ƴanbindiga suka sace ɗaliban jami'a a jihar Nasarawa, inda rahotanni suka nuna cewa ɗalibai shida aka sace, kuma suna karatu ne a tsangayar injiyanci.
A jihar Oyo hukumomi sun tabbatar da ƴanbindiga sun kai hari kan wasu makarantu guda biyu a garin Ahoro-Esinle, inda suka sace ɗalibai 46.
A watan Mayun 2026 ne mahara da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne suka sace ɗalibai sama 50 a garin Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba da ke jihar Borno.
An sace ɗaliban ne daga makarantar sakandaren gwamnati da makarantar firamaren gwamnati ta SUBEB.