Wasu 'yan bindiga sun kai samame rugar sarkin Fulani da ke gefen garin Lafiyagi, shalkwatar karamar hukumar Edun ta jihar Kwara, inda suka sace dan sarkin Fulanin da matansa biyu masu dauke da goyon jarirai, ciki har da jaririn da bai kai wata guda da haihuwa ba.
Rahotan da bbc ta wallafa a shafinta ya ce, maharan Sun kuma kashe wani mutumin garin, suka tafi da dansa shi ma.
Maharan suna neman a ba su naira miliyan dari a matsayin kudin fansa, kafin su sako mutanen da suka sace.
Al'amarin da ke kara nuna matsalar hare-haren 'yan bindiga dai ba ta bar hatta Fulani makiyaya da ke daji ba.
A cewar Ali Muhammadu Janwuro, shugaban reshen jihar Kwara na kungiyar Fulani makiyaya ta Mi-Yetti-Allah Pulako Yeso-Yeso, yan bindigar sun kai harin ne da tsakar dare, inda barayin suka dauki matan biyu suka wuce da su, sai ranar Laraba suka sake dawowoa suka sake tafiya da wasu.