Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran za a gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin.
Talbijin na channels ya rawaito cewa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wani taron tuntuba da aka gudanar a Abuja tsakanin bangaren zartarwa, Majalisar Dokoki ta Kasa da hukumomin tsaro.
Ya ce tattaunawar kafa ’yan sandan jihohi ta fara ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma yanzu an kai matakin duba gyaran kundin tsarin mulki da dokokin da za su ba da damar aiwatar da tsarin.
Gbajabiamila ya bayyana cewa yawancin masu ruwa da tsaki sun amince da bukatar kafa ’yansandan jihohi, inda ya ce muhawarar yanzu ba ta kan ko a kafa su ba ce, sai dai yadda za a samar da ingantaccen tsarin doka da gudanarwa.
Ya kara da cewa shugaba Tinubu zai karbi cikakken rahoton taron, yayin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tuntubar bangarori daban-daban domin samar da tsarin da zai inganta tsaro, tattara bayanan sirri da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin kasar nan.