Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya, ILO, ta ce yawan matasan da ba su da aikin yi ya ƙaru a duniya a shekarar 2025, musamman a ƙasashen da ke da ƙarfin tattalin arziki, a daidai lokacin da fasahar Artificial Intelligence (AI) ke ƙara yaɗuwa.
A cewar sabon rahoton ƙungiyar, yawan rashin aikin yi tsakanin matasa masu shekaru 15 zuwa 24 ya kai kashi 12.4 cikin 100 a shekarar 2025, daga kashi 12.3 cikin 100 a shekarar 2024.
Rahoton ya nuna cewa hakan na nufin kusan matasa miliyan 67 ne ba su da aikin yi a duniya.
Haka kuma, adadin matasan da ba sa aiki, ba sa zuwa makaranta, kuma ba sa samun horon sana’a ya ƙaru kaɗan, inda ya kai kashi 20 cikin 100, wanda ya shafi sama da mutane miliyan 257 a faɗin duniya.
ILO ta yi gargadin cewa raunin tattalin arziki, ƙarancin sabbin guraben aikin yi, rikice-rikicen siyasa da kuma saurin bunƙasar fasaha, musamman AI, na iya jefa duniya cikin wata sabuwar matsalar aikin yi ga matasa.
Kungiyar ta jaddada buƙatar ƙasashe su ƙara saka jari wajen ilimi, koyar da sana’o’i da ƙwarewar zamani, domin taimaka wa matasa su dace da sauye-sauyen da ke faruwa a kasuwar aiki ta duniya.