Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani sabon tsarin zuba jari da aka tsara domin jawo sabbin jarin har dala biliyan 50 a fannin hako man fetur da iskar gas daga teku mai zurfi, tare da farfaɗo da manyan ayyukan hako mai na teku da suka kwashe shekaru da dama suna dakushewa.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce sabon tsarin ya maye gurbin tattaunawar da ake yi kan kowane aiki daban da wani tsari mai fayyace ƙa’idoji da ka’idojin da suka tabbata, wanda zai bai wa masu zuba jari ƙarin tabbaci tare da ƙarfafa matsayin Najeriya wajen jawo jarin duniya.

Tsarin zai tallafa wa sabbin manyan ayyukan hako mai da iskar gas daga teku mai zurfi, inda aikin Bonga South West, wanda darajarsa ta kai kusan dala biliyan 10, zai kasance daga cikin ayyukan farko.

An aiwatar da sabon tsarin ne ta hanyar Deep Offshore Oil and Gas Projects Incentives (Tax Remission) Order, 2026, wanda ya tanadi sharuddan cancanta, hanyoyin aiwatarwa da kuma ingantaccen tsarin zuba jari na dogon lokaci, tare da kare muradun Najeriya.

Amincewar ta kuma bai wa NNPC Limited, a matsayinta na wakilin gwamnati a ƙarƙashin yarjejeniyoyin Production Sharing Contracts, damar ci gaba da yin gyare-gyaren da suka dace a cikin yarjejeniyoyin da suka cancanta domin aiwatar da sabon tsarin.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin man fetur da iskar gas, Olu Arowolo-Verheijen, ta ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sabon tsarin ya fi mayar da hankali a kai shi ne ƙarfafa ƙwarewar masana’antu na cikin gida.

Ta ce ayyukan da suka cika sharuddan za su mayar da hankali wajen gudanar da ayyuka a cikin Najeriya gwargwadon abin da ya dace ta fuskar kasuwanci da fasaha, musamman a fannonin injiniyanci, ƙera kayayyaki, jigilar kayayyaki ta ruwa, ayyukan fasaha da kula da ayyukan manyan tsare-tsare.

A cewarta, manufar ba wai ƙara zuba jari da samar da mai kaɗai ba ce, har ma da samar da guraben ayyukan yi masu buƙatar ƙwarewa, bunƙasa kamfanonin cikin gida da kuma mayar da Najeriya cibiyar gudanar da manyan ayyukan hako mai daga teku mai zurfi a Afirka.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa Ma’aikatun Tarayya na Shari’a, Kuɗi da Albarkatun Man Fetur, da Nigeria Revenue Service, NNPC Limited, Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission, Nigerian Content Development and Monitoring Board, abokan zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar, bisa gudunmawar da suka bayar wajen samar da sabon tsarin.

Shugaban ya ce ƙasashen da suka fi samun damar jawo zuba jari na dogon lokaci ba lallai ne su kasance waɗanda suka fi yawan albarkatun ƙasa ba, illa waɗanda suka fi samar da tabbaci da kyakkyawan yanayin zuba jari.

Ya ce wannan garambawul ya nuna ƙudurin gwamnatinsa na gina yanayin zuba jari da ya ginu kan ƙa’idoji bayyanannu, hukumomi masu ƙarfi da kuma haɗin gwiwa mai ɗorewa.

A cewar Shugaba Tinubu, shirin zai samar da yanayin da zai ba da damar shigowar jari, bunƙasar kasuwancin ’yan Najeriya, inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da cewa albarkatun ƙasar suna samar da fa’ida mai ɗorewa ga Najeriya baki ɗaya.