Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta tallafa wa Shirin Food for Progress na Ma’aikatar Aikin Gona ta Amurka (USDA) a Najeriya, tana mai bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen ƙarfafa sarkar darajar kamun kifi da kiwon kifaye a ƙasar.
Sakatariyar dindindin ta Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku ta Tarayya, Fatima Sugra Mahmood, ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi wata tawaga daga Partners of the Americas, wadda ke aiwatar da shirin a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Gustavo Galdo, a Abuja.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta ma’aikatar, Anastasia Ogbonna, ta fitar, Mahmood ta tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta samar da manufofi, tallafin hukumomi da kuma daidaita ayyuka da ake buƙata domin tabbatar da nasarar shirin.
A nasa jawabin, shugaban tawagar Partners of the Americas, Gustavo Galdo, ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin bunƙasa aikin noma da faɗaɗa kasuwanci a ƙasashe masu tasowa.
Ya ce mayar da hankali kan fannin kamun kifi da kiwon kifaye a Najeriya zai taimaka wajen inganta rayuwar jama'a, ƙara samun abinci mai gina jiki musamman furotin, da kuma gina tsarin samar da abinci mai ɗorewa da jure matsaloli.
Galdo ya ƙara da cewa a halin yanzu ana gudanar da binciken tushe (baseline studies) domin samar da bayanan da za su taimaka wajen tsara ayyukan da suka dace, tare da tabbatar da cewa shirin ya magance gibin da ake da shi tare da amfani da damar da ke cikin fannin kamun kifi da kiwon kifaye.