Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya tura Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, DIG Ishyaku Mohammed, jihar Osun domin jagorantar ayyukan tsaro a yayin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.

Rundunar ’Yan Sandan ta ce matakin na daga cikin shirye-shiryen da ta ɗauka domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya, tsaro da sahihanci a faɗin jihar.

DIG Ishyaku Mohammed zai jagoranci ɓangaren ’yan sanda na tsarin tsaron zaɓen tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomin Tsaro kan Zaɓe (ICCES).

Za a kuma tallafa masa da Mataimakan Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da Kwamishinonin ’Yan Sanda da aka tura zuwa yankunan sanatan jihar uku, domin kula da ayyukan tsaro, ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma tabbatar da gaggawar mayar da martani ga duk wata barazana.

Rundunar ta ce ta tanadi isasshen tsaro domin kare masu zaɓe, jami’an INEC, kayan zaɓe, rumfunan zaɓe, cibiyoyin tattara sakamako, masu sa ido da kuma ’yan jarida kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.

IGP Disu ya gargadi ’yan siyasa, magoya bayansu da duk masu shirin tayar da hankali cewa za a kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen satar akwatin zaɓe, tsoratar da masu zaɓe, daba da sauran laifukan zaɓe.

Ya kuma sake jaddada dokar hana rakiyar ’yan sanda masu ɗauke da makamai, jami’an tsaro na musamman ko wasu mutanen da ba su da izini zuwa rumfunan zaɓe ko cibiyoyin tattara sakamako tare da ’yan siyasa ko manyan baki a ranar zaɓe.

Haka kuma, rundunar ta ce ba za a bari ƙungiyoyin tsaro da jihohi suka kafa, ƙungiyoyin da ba hukumomin tsaro na yau da kullum ba, ko kamfanonin tsaro masu zaman kansu su shiga ayyukan tsaron zaɓe ba, bisa tsarin da rundunar ’yan sanda ta tanada.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar wa mazauna Osun, masu zaɓe da baƙi cewa an tanadi isasshen tsaro, tare da kira ga duk masu rajistar zaɓe da su fito su kaɗa ƙuri’unsu cikin zaman lafiya ba tare da fargaba ba.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin ƙwarewa, tsaka-tsaki, mutunta haƙƙin ɗan Adam da kuma kare tsarin dimokuraɗiyya.