Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci a sake zaɓensa a shekarar 2027, bisa la’akari da sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta aiwatar.
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman, Tunde Rahman, ne ya bayyana hakan yayin wani rangadin ayyukan gwamnati a Jihar Nasarawa.
Ayyukan Raya Ƙasa
Rahman ya ce ayyukan tituna, gadoji da cibiyoyin lafiya da tawagar ta gani a Nasarawa da Benue na daga cikin nasarorin da aka samu sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.
Ya ƙara da cewa sauye-sauyen gwamnatin tarayya sun bai wa jihohi ƙarin damar samun kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Kare Gwamnatin
Fadar Shugaban Ƙasar ta kuma mayar da martani ga sukar da ‘yan adawa ke yi wa gwamnatin Tinubu, inda ta ce ayyukan da ake gudanarwa a sassan ƙasar shaida ne kan abin da gwamnatin ta cimma.
A cewar Rahman, waɗannan ayyuka na nuna tasirin manufofin gwamnatin tarayya da kuma yadda suke taimakawa wajen inganta rayuwar jama’a.
Ziyarar Ayyuka a Nasarawa
A yayin rangadin, tawagar ta ziyarci wasu manyan ayyuka a Jihar Nasarawa, ciki har da Gadar Keffi da Mararaba, da kuma ayyukan inganta Dalhatu Araf Specialist Hospital da ke Akwanga.
Fadar Shugaban Ƙasar ta ce irin waɗannan ayyuka na daga cikin matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka wajen inganta ababen more rayuwa da harkokin kiwon lafiya a ƙasar.