Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliyar ruwa ta ba-zata a wasu sassan ƙasar, inda ta ce jihohi 13 na cikin babban haɗarin fuskantar ambaliyar tsakanin 11 zuwa 20 ga Agustan 2026.


NiMet ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, inda ta lissafa Sokoto, Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna, Nasarawa, Adamawa, Filato, Benue, Kogi, Taraba, Cross River da Akwa Ibom a matsayin jihohin da ke cikin haɗarin ambaliya.


Dalilin Gargadin

A cewar NiMet, hasashen ya dogara ne kan abubuwa da suka haɗa da yawan ruwan sama da ake sa ran samu, danshin ƙasa, ƙarfin magudanan ruwa, yanayin ƙasa da kuma yanayin madatsun ruwa.


Hukumar ta ce manufar gargadin ita ce bai wa hukumomi da al’umma damar shirya tun da wuri, ɗaukar matakan gaggawa da rage illolin ambaliyar ruwa.


Yankunan da ke cikin haɗari

NiMet ta ce ambaliyar ruwa ta ba-zata na iya faruwa musamman a wuraren da ambaliya ta saba faruwa, yankunan da suke ƙasa, birane da kuma al’ummomin da ke kusa da koguna.


Ta ce hakan na iya haifar da rufe hanyoyi, cunkoson ababen hawa da kuma kawo cikas ga harkokin sufuri.


Hukumar ta kuma yi gargadin cewa ambaliyar na iya dakatar da samar da wutar lantarki da ayyukan sadarwa na ɗan lokaci.


Illolin ambaliyar

NiMet ta ce ruwan sama mai ƙarfi na iya rage gani ga direbobi, tare da shafar zirga-zirgar ababen hawa da kuma harkokin sufurin jiragen sama.

Haka kuma, taruwar ruwa na iya lalata gonaki, amfanin gona da dabbobi, yayin da ambaliyar ruwa za ta iya lalata hanyoyi, gadoji, magudanan ruwa da sauran muhimman ababen more rayuwa.


Hukumar ta ƙara da cewa ruwan da ya tsaya bayan ambaliya na iya ƙara haɗarin yaɗuwar cututtukan da ruwa ke ɗauka, don haka ta buƙaci al’umma da hukumomi su ɗauki matakan kariya da wuri.