Dan wasan dan asalin kasar sifaniya wanda ya kasance zakakurin dan wasan duniya a gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 wanda ya gudanar a kasar America, Canada da Mexico.
Tun farko dai dan wasan ya nuna sha’awar komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, saidai yadda kungiyar taki maida hankali kansa hakan ya tilasta masa canja shawara tare da nuna sha’awar komawa Barcelona.
Wannan batu dai ya dauki hankali magoya bayan kwallon kafa ta duniya musamman na Real Madrid din da suke tunanin Barcelona na neman yi musu tsakiyar da babu ruwane a cinikin na Rodri, inda hakan ya janyo ake ta tafka muhawara a shafikan sada zumunta tsakanin magoyan kungiyoyin biyu.
A gefe guda kuma Kungiyar kwallo kafa ta Manchester city na neman cinikin yakai €70m ne saidai a safiyar yau Laraba 12/08/2026 Dan jaridar nan Fabrizio Romano ya wallafa yadda Barcelona ta kara miki tayin na €60m maimakon €50m data mika a baya.